2 Samaʼila 19:8 - Littafi Mai Tsarki8 Sa'an nan sarki ya tashi, ya zauna a dandalin ƙofar garu. Aka faɗa wa mutanensa duka, cewa, ga sarki yana zaune a dandalin ƙofar garu. Mutanensa duka kuwa suka zo suka kewaya sarki. Bayan wannan sai dukan Isra'ilawa suka gudu, kowa ya tafi gidansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |