Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 19:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Sai dukan mutanen Isra'ila suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Me ya sa mutanen Yahuza 'yan'uwanmu, suka sace ka, suka kawo sarki da iyalinsa a wannan hayin Urdun, tare da dukan mutanensa?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 19:41
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutanen Ifraimu suka yi gangami suka haye zuwa Zafon da shirin yaƙi. Suka ce wa Yefta, “Me ya sa ka haye zuwa yaƙi da Ammonawa, amma ba ka kira mu mu tafi tare da kai ba? To, yanzu za mu ƙone ka da gidanka.”


Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai.


Sojojin suka shiga birni sururu kamar waɗanda sukan shiga birni a ɓoye da kunya saboda sun gudu daga wurin yaƙi.


Da labarin abin da Isra'ilawa suke cewa, ya zo gun sarki Dawuda, sai ya aika zuwa wurin firistoci, wato Zadok da Abiyata, a faɗa musu su tambayi dattawan Yahuza abin da ya sa suka zama na ƙarshe a kan komar da sarki a gidansa.


Ya ce, “Ai, ku 'yan'uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ