Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci haka da kai ba.” Sai ya ɗibi mashi uku ya soki Absalom a ƙahon zuciya, tun yana da sauran rai, a maƙale cikin itacen oak.
Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.
Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”
Sai mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a ba ni azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba, gama a kunnuwanmu sarki ya umarce ka, kai da Abishai, da Ittayi cewa, ‘Ku lura mini da saurayin nan, Absalom.’
“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.
Dukan 'ya'yansa mata da maza suka tashi domin su ta'azantar da shi, amma ya ƙi ta'azantuwa, yana cewa, “A'a, a Lahira zan tafi wurin ɗana, ina baƙin ciki.” Haka mahaifinsu ya yi kuka dominsa.