2 Samaʼila 18:9 - Littafi Mai Tsarki9 Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 To, Absalom ya haɗu da mutanen Dawuda. Yana hawan dokinsa, kuma yayinda dokin ya kusa kai cikin rassan babban itacen oak, sai kan Absalom ya sarƙafe a kan itacen oak ɗin. Dokin ya wuce da gudu, shi kuwa ya rataye a can yana lilo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |