Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 18:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Mai tsaron ya ce, “Na ga gudun na farin kamar gudun Ahimawaz ɗan Zadok.” Sai sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana kawo kyakkyawan labari ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Sai mai tsaron ya ce, “A ganina gudu na farin, ya yi kama da gudun Ahimawaz, ɗan Zadok.” Sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana zuwa da saƙo mai kyau.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 18:27
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”


Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”


Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”


Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu, Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama. Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona, “Allahnki sarki ne!”


Jin labari mai daɗi wanda ba ka zato, yana kamar shan ruwan sanyi ne a sa'ad da ka sha rana kana jin ƙishi.


Amintaccen manzo yakan wartsakar da wanda ya aike shi, kamar ruwan sanyi yake a lokacin zafi.


Mai tsaron kuma ya ga wani mutum yana zuwa shi ma a guje, sai ya ta da murya wajen mai ƙofar garin, ya ce, “Ga wani mutum kuma yana zuwa a guje!” Sai sarki ya ce, “Shi ma labari yake kawowa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ