Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 18:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.” Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Ahimawaz ɗan Zadok ya sāke ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru, ina roƙonka bari in bi bayan mutumin Kush nan.” Amma Yowab ya ce, “Ɗana me ya sa kake so ka je? Ba ka da labarin da zai jawo maka lada.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 18:22
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.


Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.


Sa'an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa'an nan ya sheƙa a guje.


Ahimawaz ya ce, “Duk dai abin da zai faru, zan tafi.” Sai Yowab ya yardar masa ya tafi. Sa'an nan Ahimawaz ya sheƙa, ya bi ta hanyar fili, ya wuce Bahabashen.


Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?” Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa'ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”


Amma Fir'auna ya ce masa, “Me ka rasa a nan har da kake so ka koma ƙasarka?” Hadad ya ce masa, “Ka dai yardar mini kawai in tafi.” Ya kuwa koma ƙasarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ