Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 18:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa'an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 18:2
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun.


Ba na jin tsoron dubban abokan gāba Waɗanda suka kewaye ni ta kowane gefe.


Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra'ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin.


Gari na wayewa, sai Saul ya raba mutanen kashi uku, suka fāɗa wa sansanin Ammonawa da kisa tun da sassafe har rana tsaka, aka warwatsa waɗanda suka tsira ɗaya ɗaya.


Shi ma ya kwashi mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, suka yi kwanto a saura. Da ya duba, ya ga mutane suna fitowa daga cikin birnin. Ya fāɗa musu, ya karkashe su.


Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu.


Abishai, ɗan'uwan Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban jarumawan nan talatin. Sa'ad da ya girgiza mashinsa, sai da ya kashe mutum ɗari uku. Da haka ya samar wa kansa sūna tare da mutanen nan uku.


Da Yowab ya ji labari, gama har shi ya goyi bayan Adonija, ko da yake bai goyi bayan Absalom ba, sai ya gudu zuwa alfarwa ta Ubangiji, ya kama zankayen bagade.


Yowab ɗan Zeruya, shi ne shugaban sojojin. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne marubuci.


Abishai ɗan Zeruya kuwa, ya kawo wa Dawuda gudunmawa. Ya faɗa wa Bafilisten, ya kashe shi. Jama'ar Dawuda kuwa suka sa ya yi musu alkawari ba zai ƙara binsu zuwa wurin yaƙi ba. Suka ce, “Kai ne begen Isra'ila, ba mu so mu rasa ka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ