Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.
Matarsa, Zeresh kuwa, da abokansa duka suka ce, “Ka sa a shirya gungumen itace mai tsayi kamu hamsin, sa'an nan da safe ka faɗa wa sarki a rataye Mordekai a kai, sa'an nan ka tafi wurin liyafar tare da sarki da murna.” Haman kuwa ya ji daɗin wannan shawara, sai ya sa aka shirya gungumen itacen.
Zan kawo maka dukan jama'a kamar yadda akan kawo amarya a gidan angonta. Ran mutum guda kaɗai kake nema, sauran mutane duka kuwa su yi zamansu lafiya.”