2 Samaʼila 17:25 - Littafi Mai Tsarki25 Absalom ya naɗa Amasa ya zama shugaban sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan Yeter ne, Ba'isma'ile, wanda ya auri Abigail 'yar Nahash, 'yar'uwar Zeruya mahaifiyar Yowab. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗansu sojoji daga Manassa, suka tafi wurin Dawuda sa'ad da yake fita tare da Filistiyawa don su yi yaƙi da Saul. Amma Dawuda bai tafi tare da su ba, domin sarakunan Filistiyawa sun yi shawara, suka sallame shi, don kada ya juya musu gindin baka, ya nemi sulhu a wurin shugabansu Saul, da kawunansu.