Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 17:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Jonatan da Ahimawaz suna jira a En-rogel. Wata baranya takan tafi ta faɗa musu saƙo, su kuma sai su tafi su faɗa wa sarki Dawuda, don kada a gan su suna shiga birnin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Yonatan da Ahimawaz suna zaune a En Rogel. Wata baranya ce za tă je ta faɗa musu, su kuma su tafi su gaya wa Sarki Dawuda don suna tsoro kada a ga suna shiga birnin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 17:17
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga 'ya'yansu biyu suna tare da su a can, wato Ahimawaz, ɗan Zadok, da Jonatan, ɗan Abiyata. Duk abin da ka ji, ka aiko su, su zo su faɗa mini.”


Sa'an nan sarki ya ci gaba da yi wa Zadok magana, ya ce, “Ka gani, ka koma birni lafiya, kai da Abiyata tare da 'ya'yanku biyu, wato Ahimawaz ɗanka, da Jonatan, ɗan Abiyata.


Iyakar kuma ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskar kwarin ɗan Hinnon, wanda yake arewa wajen ƙarshen kwarin Refayawa. Ta kuma gangara zuwa kwarin Hinnom ta yi kudu daura da Yebusiyawa, ta gangara zuwa En-rogel.


Daga kwarin Akor ta wuce zuwa Debir ta yi wajen arewa, sa'an nan ta juya zuwa Gilgal wadda take daura da hawan Adummim wanda yake kudancin gefen kwarin. Sai ta zarce zuwa ruwan En-shemesh, ta ƙare a En-rogel.


Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza.


Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”


Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ