Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 17:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Yanzu sai ku aika wa Dawuda saƙo nan da nan ku ce masa, ‘Kada ka kwana a mashigai cikin hamada; ka tabbata ka haye ba faci, in ba haka ba sarki da dukan mutanensa za su hallaka.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 17:16
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”


Sa'ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, amma don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.


Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa, “An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”


Daga sammai Allah zai amsa mini, Zai kori waɗanda suka tasar mini, Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.


Dukan yini maƙiyana suna tasar mini, Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.


Zan hanzarta in nemi mafaka Daga iska mai ƙarfi da hadiri.”


Kada ka bar su su ce wa kansu, “Madalla! Da ma abin da muke so ke nan!” Kada ka bar su su ce, “Mun rinjaye shi!”


Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”


Ya ce wa yaron ya yi maza, kada ya tsaya. Sai yaron ya kwashe kiban ya kawo masa.


Ga shi, Zadok da Abiyata, firistoci, suna tare da kai. Duk abin da ka ji daga gidan sabon sarki, sai ka faɗa wa Zadok da Abiyata, firistoci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ