Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 16:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sa'ad da Hushai Ba'arkite, aminin Dawuda ya zo wurin Absalom, ya ce masa, “Ran sarki ya daɗe!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 16:16
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa'an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”


Sama'ila ya ce wa dukan jama'a, “Kun gan shi? Shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa, babu wani kamarsa a cikin dukan jama'a.” Jama'a duka kuwa suka yi sowa suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”


Gama yau ɗin nan ya tafi ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Yowab shugaban sojoji, da Abiyata firist. Ga shi, suna ci suna sha tare da shi, suna cewa, ‘Ran sarki Adonija ya daɗe.’


Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”


Sai Daniyel ya ce wa sarki, “Ran sarki ya daɗe!


Sa'an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe!


Da sarauniya ta ji maganganun sarki da na manyan fādawansa, sai ta shiga babban ɗakin da ake liyafar, ta ce, “Ran sarki, ya daɗe! Kada ka firgita, kada kuma fuskarka ta turɓune.


Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.”


a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’


Hushai, abokin Dawuda kuwa, ya isa Urushalima daidai lokacin da Absalom yake shiga.


Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, ‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.’ Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.


Da Dawuda ya hau kan dutse inda ake yi wa Allah sujada, sai ga amininsa Hushai Ba'arkite, da ketacciyar riga, da ƙura a kansa, ya zo ya taryi Dawuda.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ