2 Samaʼila 16:11 - Littafi Mai Tsarki11 Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.