A yau ina da shekara tamanin cif. Ba zan iya in rarrabe abu mai daɗi da marar daɗi ba. Ba kuma zan iya ɗanɗana daɗin abin da nake ci ko abin da nake sha ba. Ba zan iya jin daɗin muryar mawaƙa ba. Zan zamar maka kaya kurum, ranka ya daɗe.
Amma in za ka koma cikin birnin, ka ce wa Absalom, ‘Ya sarki, zan zama baranka kamar yadda na zama baran mahaifinka a dā. Haka zan zama baranka.’ Ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.