Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 15:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Dawuda yana tafe ba takalmi a ƙafarsa, ya rufe kansa, yana ta kuka, sa'ad da yake hawan Dutsen Zaitun, dukan mutane kuma da suke tare da shi suka rufe kawunansu, suna hawa, suna kuka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Amma Dawuda ya ci gaba yana hawan Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake tafiya; kansa a rufe, kuma babu takalma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suna ta kuka yayinda suke haurawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 15:30
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'an nan Mordekai ya koma ƙofar sarki, Haman kuwa ya gaggauta zuwa gidansa, yana baƙin ciki, kunya ta rufe shi.


Sarki ya rufe fuskarsa, ya yi kuka da ƙarfi, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ya Absalom, ɗana, ɗana!”


Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi.


Ka yi ajiyar zuciya a hankali, kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka, ka sa takalmanka, kada ka ja amawali, kada kuma ka ci abincin masu makoki.”


Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.


Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.


Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya.


Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.


Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.


Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka,


Da ya zo gab da gangaren Dutsen Zaitun, sai duk taron almajiran suka ɗauki murna, suna yabon Allah da murya mai ƙarfi saboda duk mu'ujizan da suka gani.


Da ya kusato Betafaji da Betanya, a wajen dutsen da ake kira Dutsen Zaitun, ya aiki almajiransa biyu,


“Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.


A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.


Me ya sa nake baƙin ciki? Me ya sa nake damuwa? Zan dogara ga Allah, Zan ƙara yabonsa, Mai Cetona, Allahna.


Dare da rana ina kuka, Hawayena kaɗai su ne abincina, A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata, “Ina Allahnka?”


Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.


Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan 'ya'yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ