28 Ni kuwa zan dakata a nan bakin jeji har na sami labari daga gare ka.”
28 Zan kuwa jira a mashigai a hamada, sai na ji daga gare ku.”
Yanzu sai ka aika da sauri a faɗa wa Dawuda, kada ya kwana a bakin jeji a daren yau, amma ya haye don kada a hallaka shi tare da mutanensa.”
Dukan ƙasar ta yi ta kururuwa sa'ad da mutane suka tashi. Sarki ya haye rafin Kidron, mutane kuma suka haye, suka nufi jeji.
Ahitofel ya kuma ce wa Absalom, “Bari in zaɓi mutum dubu goma sha biyu (12,000), mu tafi mu bi Dawuda da daren nan.
Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?” Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da 'ya'yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”
Sa'ad da Isra'ilawa suke zaune a Gilgal, sai suka yi Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan, da maraice, a filayen Yariko.
Zadok da Abiyata kuwa suka ɗauki akwatin alkawari suka koma Urushalima, suka zauna a can.