2 Samaʼila 15:24 - Littafi Mai Tsarki24 Sai ga Abiyata ya zo, sai kuma ga Zadok ya zo tare da dukan Lawiyawa, ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka ajiye akwatin har dukan mutane suka gama fita daga birnin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202024 Zadok yana nan tare da su, kuma dukan Lawiyawan da suke tare da shi kuwa suna ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka sauke akwatin alkawarin Allah, Abiyatar ya miƙa hadaya sai da mutane suka gama fita daga birnin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.