Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 15:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Absalom yakan tashi da wuri, ya tsaya a kan hanyar da take shiga ƙofar garin. Idan wani mai kai ƙara ya zo wurin sarki don shari'a, Absalom yakan kira shi, ya ce, “Daga ina kake?” Idan mutumin ya faɗa masa garin da ya fito daga cikin Isra'ila,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya a gefen hanyar shigar ƙofar birni. Duk sa’ad da wani ya zo da ƙara don a kai gaban sarki yă yi shari’a, Absalom yakan kira shi yă ce, “Daga wane gari ka fito?” Sai mutumin yă amsa yă ce, “Bawanka ya fito a ɗaya daga cikin kabilan Isra’ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 15:2
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da gari ya waye sai duk manyan firistoci da shugabannin jama'a suka yi shawara a kan Yesu su kashe shi.


Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani.


Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci, Da dare kuma ya yi fashi.


Sa'an nan sarki ya tashi, ya zauna a dandalin ƙofar garu. Aka faɗa wa mutanensa duka, cewa, ga sarki yana zaune a dandalin ƙofar garu. Mutanensa duka kuwa suka zo suka kewaya sarki. Bayan wannan sai dukan Isra'ilawa suka gudu, kowa ya tafi gidansa.


Bo'aza fa ya tafi, ya zauna a dandalin ƙofar gari. Sai ga wani daga cikin waɗanda hakkinsu ne su ɗauki Rut, shi ne kuwa wanda Bo'aza ya ambata, ya iso. Bo'aza kuwa ya ce masa, “Ratso nan, wāne, ka zauna.” Sai ya ratsa, ya zauna.


Suka yi ta yi wa jama'a duka shari'a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.


A sa'ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.”


Da surukin Musa ya ga yadda Musa yake fama da jama'a, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa jama'a? Don me kake zaune kai kaɗai, mutane kuwa na tsattsaye kewaye da kai, tun daga safe har zuwa maraice?”


Hamor kuwa da ɗansa Shekem, suka je dandali a bakin ƙofar birni, suka yi wa mutanen birninsu magana, suka ce,


“Idan aka kawo muku shari'a mai wuyar yankewa a ɗakin shari'arku, ko ta kisankai ce, ko ta jayayya ce, ko ta cin mutunci ce, ko kowace irin shari'a mai wuyar yankewa, sai ku tashi, ku tafi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.


Su kuwa suka ce masa, “Idan za ka nuna wa jama'ar nan alheri, ka daɗaɗa musu rai, ka kuma yi musu magana mai daɗi, za su zama barorinka har abada.”


“Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ