Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 15:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Mutum ɗari biyu daga Urushalima suka raka Absalom. An gayyace su a matsayin baƙi, suka kuwa tafi cikin rashin sani, ba su san wani abu game da al’amarin ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 15:11
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”


Yau ne na fara roƙar masa Allah? A'a, kada dai sarki ya zargi baransa ko gidan mahaifina duka, gama baranka bai san kome a kan wannan ba.”


“Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.


Mutum mai hankali, in ya ga wahala tana zuwa yakan kauce mata, amma shashasha yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.


Wawa yakan gaskata kowane abu, amma mai la'akari yana lura da takawarsa.


Ba shi ya faɗa mini, ‘Ita 'yar'uwata ce’ ba? Ba ita kanta kuma ta ce, ‘Shi ɗan'uwana ne’ ba? Cikin mutunci da kyakkyawan nufi na aikata wannan.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ