Da jin haka sai sarki ya ce wa Ziba, “Dukan abin da yake na Mefiboshet ya zama naka.” Ziba kuma ya rusuna ya yi godiya ya ce, “Bari in zama majidaɗin ubangijina, sarki.”
Yanzu kuwa dukan dangi sun tasar mini, suna cewa, in ba da ɗayan wanda ya kashe ɗan'uwansa domin su kashe shi saboda ran ɗan'uwansa da ya kashe. Wato za su hallaka magāji ke nan, ta haka za a yi biyu babu ke nan, su bar mijina ba suna ko zuriya a duniya.”