Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.
(Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)
Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”