Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 14:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 14:22
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

'Ya'yanta sukan tashi su gode mata, mijinta kuma yana yabonta.


Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba, Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,


Waɗanda suka ji labarina sukan sa mini albarka, Waɗanda suka gan ni sukan yi na'am da ni.


Jama'a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.


Sa'an nan dukan jama'a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.


Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”


Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.” Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.”


Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.


Yusufu kuwa ya shigo da Yakubu mahaifinsa, ya tsai da shi a gaban Fir'auna, Yakubu kuwa ya sa wa Fir'auna albarka.


Sa'an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”


Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.


Sa'ad da macen nan da ta zo daga Tekowa ta isa gaban sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma. Sa'an nan ta ce, “Ya sarki, ka yi taimako.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ