Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 14:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Gama sarki zai ji, ya cece ni daga hannun mutumin nan da zai hallaka ni tare da ɗana daga cikin jama'ar Allah.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Wataƙila sarki zai yarda yă ceci baiwarsa daga hannun mutumin nan da yake ƙoƙari yă hallaka ni da ɗana daga gādon da Allah ya ba mu.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 14:16
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’


Gama rabon Ubangiji shi ne jama'arsa, Yakubu shi ne rabon gādonsa.


Saboda mutane sun tsorata ni shi ya sa na zo in faɗa wa ubanjijina, sarki. Na kuwa yi tunani na ce, ‘Zan tafi in faɗa wa sarki, watakila sarki zai amsa roƙona.


Garinmu lafiyayye ne, amintacce ne kuma a cikin Isra'ila. Me ya sa kake so ka hallaka garin? Kana so ka rushe abin da yake na Allah?”


Yakan ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi, Da waɗanda suke da bukata, Da waɗanda ba a kula da su.


Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ