Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 13:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Yonadab kuwa ya ce masa, “Kwanta a gadonka ka yi kamar kana ciwo, lokacin da mahaifinka ya zo domin ya duba ka, sai ka ce masa, ‘A bar ƙanwata Tamar ta zo ta ba ni abinci, ta riƙa shirya abincin a idona, don in gani in kuma riƙa ci daga hannunta.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Yonadab ya ce, “Je gado ka kwanta kamar ba ka da lafiya. Sa’ad da mahaifinka ya zo ganinka, sai ka ce masa, ‘Ina so ƙanuwata Tamar tă kawo mini wani abu in ci. Bari tă shirya abincin a gabana don in ganta, in kuma ci daga hannunta.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 13:5
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka, yanzu ku da majalisa ku shaida wa shugaban soja ya kawo muku shi, kamar kuna so ne ku ƙara bincika maganarsa sosai, mu kuwa a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso.”


Ɗana idan ka bar yin nazari za ka manta da abin da ka riga ka koya.


Ahitofel kuwa ya ce wa Absalom, “Ka shiga ka kwana, da ƙwarakwaran tsohonka waɗanda ya bar su su lura da gidan. Dukan Isra'ilawa za su sani ba shiri kuma tsakaninka da tsohonka. Dukan masu goyon bayanka kuma za su ƙara ƙarfafa.”


Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?” Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan'uwana Absalom.”


Amnon kuwa ya kwanta, ya yi kamar yana ciwo. Sa'ad da sarki ya zo duba shi, sai Amnon ya ce wa sarki, “Ina roƙo a sa ƙanwata, Tamar, ta zo ta toya mini waina a inda nake, ta riƙa ba ni da hannunta ina ci.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ