Absalom ya ce wa Yowab, “Har sau biyu na aika maka domin ka zo in aike ka wurin sarki, ka tambaya mini, ‘Ko me ya sa na komo daga Geshur?’ Da ma ina can har yanzu, ai, da ya fi mini. Yanzu har ni in tafi wurin sarki, idan ina da laifi, to, ya kashe ni.”
Sa'an nan ta ce, “To, me ya sa ka yi wa jama'ar Allah irin wannan abu? Gama bisa ga maganar bakinka, ya sarki, ka hukunta kanka tun da yake sarki bai yarda ɗansa ya komo gida ba.
Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.