Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 13:37 - Littafi Mai Tsarki

37 Amma Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai, ɗan Ammihud, Sarkin Geshur. Dawuda kuwa ya yi makokin Amnon ɗansa kwana da kwanaki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

37 Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 13:37
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.


Absalom ya ce wa Yowab, “Har sau biyu na aika maka domin ka zo in aike ka wurin sarki, ka tambaya mini, ‘Ko me ya sa na komo daga Geshur?’ Da ma ina can har yanzu, ai, da ya fi mini. Yanzu har ni in tafi wurin sarki, idan ina da laifi, to, ya kashe ni.”


Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.


Absalom kuwa ya gudu. Sa'an nan sojan da yake tsaro a wannan lokaci ya ga ɗumbun mutane suna tahowa daga hanyar Horonayim, wajen gefen dutse.


Yana gama magana ke nan, sai ga 'ya'yan sarki sun iso. Suka yi ta kuka da ƙarfi. Sarki kuma da dukan fādawansa suka yi kuka mai tsanani.


Sa'an nan ta ce, “To, me ya sa ka yi wa jama'ar Allah irin wannan abu? Gama bisa ga maganar bakinka, ya sarki, ka hukunta kanka tun da yake sarki bai yarda ɗansa ya komo gida ba.


Gama na yi wa'adi sa'ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa'adi cewa, ‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ