Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 13:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Amma Absalom bai tanka wa Amnon da wata magana ta alheri ko ta mugunta ba, gama yana ƙin Amnon saboda ya yi wa Tamar ƙanwarsa faɗe.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Absalom kuwa bai yi wa Amnon wata magana ta alheri ko ta mugunta ba; ya ƙi jinin Amnon domin ya ci mutuncin ƙanuwarsa Tamar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 13:22
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.”


Kowa da yake ƙin dan'uwansa, mai kisankai ne. Ƙun kuwa sani ba mai kisankan da yake da rai madawwami a zauna tare da shi.


Laban da Betuwel suka amsa suka ce, “Wannan al'amari daga Ubangiji ne, ba mu da iko mu ce maka i, ko a'a.


Mai ƙin ɗan'uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.


Kowa ya ce yana a cikin haske, yana kuwa ƙin ɗan'uwansa, ashe, a duhu yake har yanzu.


Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da yanke, da kowace irin ƙeta.


In kun husata, kada ku yi zunubi, kada ma fushinku ya kai faɗuwar rana,


“In ɗan'uwanka ya yi maka laifi, sai ka je, ka gaya masa laifinsa, kai da shi, ku kaɗai. In ya saurare ka, to, kā maido da ɗan'uwanka ke nan.


Ka kame fushinka, Gama wawa ne yake cike da fushi.


Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye ta da maganar bakinsa, yana kuma ƙunshe da munafunci.


Idan kai da maƙwabcinka kun saɓa, ku daidaita a tsakaninku, kada a tona asiri.


Mutumin da yake faɗar ƙarairayi maƙiyi ne, dukan wanda yake baza jitajita wawa ne.


Ina da iko in yi maka lahani, amma Allah na mahaifinka, ya yi magana da ni a daren jiya, yana cewa, ‘Ka kula fa kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.’


Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.


kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne.


Da Dawuda sarki ya ji wannan, sai ya husata ƙwarai.


Ko da yake kila zai ɓoye ƙiyayyarsa, duk da haka muguntarsa za ta bayyana ga mutane.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ