'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.
Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila?
Absalom wanta ya tambaye ta, ya ce, “Ko Amnon wanki ya ɓata ki? To, yi shiru, ƙanwata, shi wanki ne, kada ki damu da yawa.” Tamar kuwa ta zauna a kaɗaice a gidan Absalom wanta.
A lokacin da Isra'ila yake zaune a ƙasar, Ra'ubainu ya je ya kwana da Bilha kwarkwarar mahaifinsa, Isra'ila kuwa ya sami labari. 'Ya'yan Isra'ila, maza, su goma sha biyu ne.