Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.
Na kuma ba ka gidan ubangidanka da matansa. Banda wannan kuma na ba ka gidan Isra'ila da na Yahuza. Da a ce wannan ya yi maka kaɗan, da na ƙara maka kuma kamar haka.
Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.
Amma talakan ba shi da kome sai 'yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi renonta, ta yi girma a wurinsa, tare da 'ya'yansa. Takan ci daga cikin ɗan abincinsa, ta kuma sha daga cikin abin shansa, ta kwanta a ƙirjinsa. Ta zama kamar 'ya a gare shi.