Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 12:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?” Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Dawuda ya gane bayinsa suna wa juna raɗan wani abu, sai ya gane yaron ya mutu. Sai ya ce, “Yaron ya rasu ko?” Suka ce, “I, ya rasu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 12:19
4 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”


Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa'an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci.


Sai zuciyar sarki ta koma kan Absalom, gama ya haƙura a kan Amnon da yake ya riga ya rasu.


Amma 'yan'uwa, ba mu so ku jahilta game da waɗanda suka yi barci, don kada ku yi baƙin ciki kamar yadda sauran suke yi, marasa bege.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ