2 Samaʼila 12:18 - Littafi Mai Tsarki18 An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 A rana ta bakwai sai yaron ya rasu. Barorin Dawuda suka ji tsoro su gaya masa cewa yaron ya mutu, gama sun yi tunani cewa, “Yayinda yaron yake da rai, mun yi magana da Dawuda bai ji mu ba. Yaya za mu gaya masa yaron ya mutu? Ai, zai yi wa kansa ɓarna.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |