5 Matar kuwa ta yi juna biyu, sai ta aika a faɗa wa Dawuda, cewa, tana da ciki.
5 Matar ta yi ciki, ta kuwa aika wa Dawuda, tana cewa, “Ina da ciki.”
“Idan aka iske wani yana kwance da matar wani, sai a kashe dukansu biyu, wato mutumin da matar. Haka za ku kawar da mugunta daga Isra'ila.
Hasalar miji mai kishi babu irinta, ramawarsa ba dama.
“Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar.
Dawuda kuwa ya aika wurin Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya Bahitte.” Yowab kuwa ya aika da Uriya wurin Dawuda.