sai ya aika zuwa Tekowa a kira masa wata mace mai hikima. Da ta zo, ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki, ki sa rigunan makoki, kada ki shafa mai. Ki yi kamar wadda ta yi kwanaki da yawa tana makokin rasuwar wani.
Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara.
Isuwa dai ya ƙi jinin Yakubu saboda albarkar da mahaifinsa ya sa masa. Sai Isuwa ya ce a ransa, “Kwanakin makoki domin mahaifina suna gabatowa, sa'an nan zan kashe Yakubu ɗan'uwana.”
Sa'ad da suka kai farfajiyar masussukar Atad, wanda yake wajen Urdun, a nan ne fa suka yi makoki, da babban makoki da baƙin ciki mai zafi. Aka kuwa yi kwana bakwai ana makokin mahaifinsa.
Dawuda ya ce wa manzon, “Je ka ka faɗa wa Yowab kada wannan abu ya dame shi, ai, takobi ba ya tarar wanda zai kashe. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku faɗa masa har ku ragargaza shi. Ka ƙarfafa Yowab.”