18 Sai Yowab ya aika aka faɗa wa Dawuda labarin yaƙin.
18 Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin.
Mutanen garin suka fito suka yi yaƙi da Yowab. Suka kashe waɗansu daga cikin sojojin Dawuda. Uriya Bahitte, shi ma aka kashe shi.
Ya ce wa manzo, “Bayan da ka gama faɗa wa sarki labarin yaƙin duka, idan sarki ya husata, har ya ce maka, ‘Me ya sa kuka tafi yaƙi kurkusa da garin? Ba ku sani ba za su tsaya a gefen garu daga ciki su yi harbi?
Da aka faɗa masa cewa an kawo kawunan 'ya'yan sarki, sai ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar garin har safiya.”