Talakawa kamar shaƙar numfashi suke, Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani. Ko an auna su a ma'auni, sam ba su da nauyin kome, Sun fi numfashi shakaf.
Me ya sa ka raina maganar Ubangiji, har da ka aikata mugun abu haka a gabansa? Ka kashe Uriya Bahitte ta hannun Ammonawa, ka ɗauki matarsa ta zama matarka.