7 Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab da dukan rundunar jarumawan.
7 Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.
Da Ammonawa suka ga sun sa Dawuda ya yi gāba da su, suka yi sufurin Suriyawan Bet-rehob da na Zoba, mutum dubu ashirin (20,000), suka kuma yi sufurin Sarkin Ma'aka da mutanensa dubu ɗaya, da mutanen Ish-tobi dubu goma sha biyu (12,000).
Ammonawa suka fita suka ja dāgar yaƙi a ƙofar garin, amma Suriyawan Zoba da na Rehob, da mutanen Ish-tobi da na Ma'aka suka ja tasu dāgar a karkara.