Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu'o'in mutanena, amma ba su yi addu'a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al'ummar ba ta yi addu'a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’
Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”
Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu.
Mutumin kuwa ya amsa ya ce, “Ya zama fa ina kan dutsen Gilbowa, sai ga Saul ya jingina a māshinsa. Karusai da mahayan dawakan abokan gāba sun rutsa shi.