Da Elisha ya kamu da ciwon ajali, sai Yehowash Sarkin Isra'ila ya tafi wurinsa, ya yi kuka a gabansa, yana cewa, “Ubana, Ubana, karusar Isra'ila da mahayan dawakanta!”
Elisha kuwa ya gani, ya yi kuka yana cewa, “Ubana, ubana! Mai ikon tsaron Isra'ila! Ka tafi ke nan!” Bai kuwa ƙara ganin Iliya ba. Da baƙin ciki Elisha ya kama tufafinsa ya kece.