25 “Jarumawa sun fāɗi, An kashe su a bakin dāga. Jonatan na kwance matacce a tuddai.
25 “Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku.
“An kashe darajarki, ya Isra'ila, a kan tuddanki! Jarumawan sojojinmu sun fāɗi!
“Jarumawa sun fāɗi, Makamansu ba su da sauran amfani.”
Rawani ya fāɗi daga kanmu, Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!
Amma mutanen Zabaluna da na Naftali Suka kasai da ransu a bakin dāga.
“Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul! Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa, Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.