Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 9:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Su kuwa za su yi muku addu'a, su yi ɗokin ganinku saboda alherin Allah marar misaltuwa da ya yi muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 9:14
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu.


Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.


Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi.


To, 'yan'uwa, muna so mu sanar da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikilisiyoyin Makidoniya,


Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya.


Ku ma sai ku taimake mu da addu'a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu'o'i masu yawa.


Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa.


Ina gaya muku, ku yi abokai ta dukiya, ko da yake aba ce wadda take iya aikata mugunta, don sa'ad da ta ƙare su karɓe ku a gidaje masu dawwama.


Mutane sukan la'anci mai ɓoye hatsi, yana jira ya yi tsada, amma sukan yabi wanda yake sayar da nasa.


Haka kuwa barorin Absalom suka kashe Amnon yadda Absalom ya umarta. Sauran 'ya'yan sarki kuwa suka tashi, kowa ya hau alfadarinsa, ya gudu.


Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na'am da bisharar Almasihu, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.


Godiya tā tabbata ga Allah saboda baiwarsa da ta fi gaban a faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ