Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 8:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Titus kuwa, ai, abokin tarayyata ne, abokin aikina kuma game da al'amuranku. 'Yan'uwan nan namu kuwa, ai, manzanni ne na ikilisiyoyi, masu ɗaukaka Almasihu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 8:23
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma na ga lalle ne in aiko muku da Abafaroditas ɗan'uwana, abokin aikina, abokin famana kuma, wanda kuka aiko ya yi mini ɗawainiya.


Saboda haka in ka ɗauke ni a kan abokin tarayya, to, sai ka karɓe shi kamar yadda za ka karɓe ni.


Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.


Domin haka ya kamata mu karɓi irin mutanen nan, mu ɗau nauyinsu, domin mu zama abokan aiki da su a kan gaskiya.


haka kuma Markus, da Aristarkus, da Dimas, da Luka, abokan aikina, suna gaishe ka.


Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.


Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,


Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.


Na roƙi Titus ya je, na kuma aiko ɗan'uwan nan tare da shi. To, Titus ya cuce ku ne? Ashe, ba Ruhu ɗaya yake bi da mu ba, ni da shi? Ba kuma hanya ɗaya muke bi ba?


ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikilisiyoyi sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.


Godiya tā tabbata ga Allah wanda ya sa tsananin kula da ku a zuciyar Titus, kamar yadda nake yi.


Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus,


haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”


Sai suka yafato abokan aikinsu a ɗaya jirgin su zo su taimake su. Suka kuwa zo, suka ciccika jiragen nan duka biyu kamar sa nutse.


Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi.


Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.


Ga shi, mun aiko ɗan'uwan nan tare da shi, wanda ya yi suna wajen yin bishara a dukan ikilisiyoyi,


Muna kuma aiko da ɗan'uwanmu tare da su, wanda sau da yawa muka tabbatar da himma tasa ta hanya iri iri, yanzu kuma ya fi koyaushe himma, domin amincewa da ku da yake yi ƙwarai da gaske.


domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.


zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka. Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ