Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 8:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Wato, muna gudun kada kowa yă zarge mu a kan kyautan nan da ake yi hannu sake, wadda muke kasaftawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 8:20
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima.


Abin da nake yi kuwa, shi zan riƙa yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.


Sa'ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima.


Saboda haka kada abin da ka ɗauka kyakkyawa ya zama abin zargi ga waɗansu.


“Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.


Ba a nemi lissafin kuɗin a wurin mutanen da aka ba su kuɗin don su biya ma'aikatan ba, gama su amintattu ne.


ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikilisiyoyi sun zaɓe shi ya riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu.


Niyyarmu ce mu yi abubuwan da suke daidai, ba wai a gaban Ubangiji kaɗai ba, har ma a gaban mutane.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ