2 Korintiyawa 7:8 - Littafi Mai Tsarki8 Ko da na ɓata muku rai a game da wasiƙar da dā na rubuto muku, ba na baƙin ciki da haka, ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙar nan ta ɓata muku rai, ko da yake dai zuwa ɗan lokaci kaɗan ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Ko da na ɓata muku rai ta wurin wasiƙata, ba na baƙin ciki da haka. Ko da yake dā kam na yi baƙin ciki, don na lura wasiƙata ta ɓata muku rai, amma na ɗan lokaci ne kawai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.