Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 7:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Saboda haka ne zukatanmu suka ƙarfafa. Banda ƙarfafa zukatanmu kuma, har wa yau mun ƙara farin ciki ƙwarai, saboda farin cikin Titus, don dukanku kun wartsakar da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ta wurin wannan duka, muka sami ƙarfafawa. Ban da ƙarfafawar da muka samu, mun ji daɗi ƙwarai saboda yadda muka ga farin cikin Titus, domin ruhunsa ya sami wartsakewa daga gare ku duka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 7:13
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus,


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.


har in Allah ya yarda in iso wurinku da farin ciki, mu wartsake tare.


Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.


Ya ɗan'uwana, ka yarda in sami wata fa'ida a gare ka saboda Ubangiji! Ka sanyaya mini zuciya saboda Almasihu.


Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba.


Saboda haka na ɗokanta ƙwarai in turo shi domin ku yi farin cikin sāke ganinsa, ni kuma in rage baƙin cikina.


Ransa kuma yana a gare ku fiye da dā ƙwarai, duk sa'ad da yake tunawa da biyayyarku, ku duka, da kuma yadda kuka yi na'am da shi a cikin halin bangirma tare da matsananciyar kula.


duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, domin ban tarar da ɗan'uwana Titus a can ba, saboda haka, sai na yi bankwana da su, na zarce na tafi Makidoniya.


Na rubuto muku haka ne, don kada in na zo, waɗanda ya kamata su faranta mini rai, ya zamana sun sa ni baƙin ciki. Domin na amince da ku duka, cewa farin cikina naku ne ku duka.


Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.


Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.


Don ko da na gaya masa cewa, ina 'yar taƙama da ku, ban kunyata ba. Kamar yadda duk abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka kuma taƙamarmu da ku a idon Titus ma ta zama gaskiya.


Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ