Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 7:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 7:10
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,


Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”


Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.” Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.


Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’


Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”


Allah kuwa ya ga abin da suka yi, ya ga yadda suka bar mugayen ayyukansu, sai ya dakatar da nufinsa, bai hallaka su ba.


Kun dai sani daga baya, da ya so yă gāji albarkar nan, sai aka ƙi shi, domin bai sami hanyar tuba ba, ko da yake ya yi ta nemanta har da hawaye.


Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da baƙin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.


Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?” Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”


Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda 'ya'yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.


Ina tsoro kada in na sāke zuwa, Allahna ya ƙasƙanta ni a gabanku, in kuma yi baƙin ciki saboda waɗansu da yawa da suka yi zunubi a dā, ba su kuwa tuba da aikinsu na lalata ba, da fasikancinsu, da fajircinsu da suka aikata.


Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.


Sai dukan mutane da dabbobi su sa tufafin makoki. Kowa ya roƙi Allah da gaske, kowa kuma ya bar mugayen ayyukan da yake yi.


Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.


Da kuka za su komo. Da ta'aziyya zan bishe su, in komar da su, Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan ruwa, A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba za su yi tuntuɓe ba. Gama ni uba ne ga Isra'ila, Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”


Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa'ad da yake ciwo, amma idan ya karai, to, tasa ta ƙare.


Wahaltaccen mutum a ko yaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.


Sa'ad da mutum yake murna yakan yi murmushi, amma sa'ad da yake baƙin ciki yakan yi nadama.


Ahab ya koma gida da baƙin ciki da rai a ɓace saboda abin da Nabot Bayezreyele ya faɗa masa. Ahab ya kwanta a gadonsa, ya mai da fuskarsa bango ya ƙi cin abinci.


Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.


Sai ya ce masa, “Ya ɗan sarki, me ya sa kake damuwa kowace rana? Ba za ka faɗa mini ba?” Sai Amnon ya ce masa, “Na jarabtu ne da Tamar ƙanwar ɗan'uwana Absalom.”


Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”


Na hurta zunubaina, Sun cika ni da taraddadi.


Baƙin ciki ya fi dariya, Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.


Amma a yanzu kam, ina farin ciki, ba don kun yi baƙin ciki ba, sai dai don baƙin cikinmu ya sa ku tuba, don kun yi baƙin ciki irin wanda Allah yake so. Saboda haka, ba ku yi hasarar kome a sanadinmu ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ