Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba? Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.
Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”
Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.
Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”
Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”