13 Ina roƙonku kamar 'ya'yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
13 A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ’ya’yana, ku ma ku saki zuciya da mu.
Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji 'ya'yana suna bin gaskiya.
Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada mu nuna ƙauna da fatar baki kawai, sai dai da aikatawa da kuma gaskiya.
Ya ku 'ya'yana ƙanana, kada fa kowa ya ɓad da ku. Shi wanda yake aikata adalci, mai adalci ne, kamar yadda Almasihu mai adalci ne.
Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci.
Domin kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da 'ya'yansa ne, muna ta'azantar da ku, muna kuma ƙarfafa muku umarnin, cewa
Ina roƙonku, ya ku 'yan'uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba.
Don haka ina dai gaya muku, kome kuka roƙa da addu'a, ku gaskata cewa samamme ne, za ku kuwa samu.
Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar. Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku.
Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!
Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka, Gama za ka ƙara mini fahimi.