Saboda haka, ina yi maka shawara ka sayi zinariya a guna, wadda aka tace da wuta, don ka arzuta, da kuma fararen tufafi da za ka yi sutura, ka rufe tsiraicinka don kada ka ji kunya, da kuma man shafawa a ido don ka sami gani.
(“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)
Sa'ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, amma don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa.