An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!
Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.
Tun da yake muna da ruhun bangaskiya iri ɗaya da na wanda ya rubuta wannan, “Na gaskata, saboda haka na yi magana,” to, mu ma mun gaskata, saboda haka kuma muke magana.