Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ba domin mun isar wa kanmu ba ne, har da za mu ce mu ne muke gudanar da wani abu, a'a, iyawarmu daga Allah take,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ba mu da wani abin da za mu nuna cewa da iyawarmu ne muke aikin nan. Iyawarmu daga wurin Allah ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 3:5
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.


Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.


Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.


Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.


Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba.


Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


Ni na yi shuka, Afolos ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar.


Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba.


Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.


Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.


Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?


Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya alkawarta. Amma ku dakata a birni tukuna, har a yi muku baiwar iko daga Sama.”


Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.”


Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.


Ba zan kuskura in faɗi kome ba, sai abin da Almasihu ya aikata ta wurina, a wajen sa al'ummai biyayya ta wurin maganata da aikina,


Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ